Isa ga babban shafi
ICC

Shugabannin Afrika na nazarin ficewa kotun ICC

Kungiyar Tarayyar Afrika na nazarin janye wakilcinta daga kotun hukunta laifukan yaki ta ICC bayan shugabannin Nahiyar sun zargi kotun da mayar da hankalinta kawai a Afrika.

Shugabar Hukumar Tarayyar Afrika Dlamini-Zuma da Shugaban Chadi Idriss Deby
Shugabar Hukumar Tarayyar Afrika Dlamini-Zuma da Shugaban Chadi Idriss Deby REUTERS
Talla

Shugaban Chadi kuma Sabon shugaban Tarayyar Afrika Idriss Deby ya soki kotun da ya kira a matsayin karen farautar kasashen yammaci.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Deby yace ana aikata tabargaza da keta hakkin bil’adama a wurare da dama amma babu wanda ya damu.

Kasar Kenya ce dai ta gabatar da bukatar ficewa daga kotun ICC, kuma yanzu shugabannin kasashen na Afrika za su yi nazari tare da fito da hanyoyin da za su janye wakilcinsu daga Kotun.

Tsohon Shugaban Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo ya kasance shugaban kasa na farko da ya gurfana gaban kotun ICC.

Tun kafa kotun a 2002 domin hukunta laifukan yaki, kotun ta mayar da hankali a Afrika kamar yadda ta kaddamar da bincike a kasashen Sudan da Libya da Uganda da Mali da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo.

Amma da dadewa Kotun na kare kanta inda Babbar mai gabatar da kara a kotun Fatou Bensouda ‘yar kasar Gambia a Nahiyar Afrika ke cewa da bukatun kasashen ne kotun ke aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.