Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Faransa za ta janye dakarunta daga Afrika ta tsakiya

Gwamnatin Faransa ta bayyana matakin janye dakarunta daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya yayin da ta ke ci gaba da kokarin yaki da ta’addanci a kasarta.

Dakarun wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya
Dakarun wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya AFP PHOTO/STR
Talla

Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drien ya fada wa kafafen yada labaran kasar cewa, suna shirin kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da aka kaddamar a shekarar 2013 a dai dai lokacin da dubban jama’a ke mutuwa saboda rikicin kasar na kabilanci.

Faransa ta aika da dakarun 2,500, inda akasarinsu aka girke su a babban birnin Bangui domin tallafawa dakarun wanzar da zaman lafiya kimanin 10,000 na majalisar Dinkin Duniya.

Sakamakon lafawar tarzoma a Afrika ta Tsakiya gami da zaben shugaban kasar da ke tafe, Faransa na son dawo da dakarunta gida saboda tana bukatar su taimaka wajan fada da mayakakn jihadi a gabaas ta Tsakiya da wasu sassan Afrika .

Faransa kuma na bukatan karfafa aikin sojinta a tsakiyar kasar, inda ta girke kimanin dakaru 10,000 domin kare lafiyar jama’a bayan harin da kungiyar ISIS ta kai birnin Paris a bara, inda ta kashe mutane 130.

Sai dai ana zargin dakarun Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya da cin zarafin kananan yara mata ta hanyar yin lalata da su a Jamhuriyar Afrika Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.