Isa ga babban shafi
Syria-MDD

'Yan adawar Syria sun amince su shiga tattaunawar sulhu a Geneva

A karon farko babban mai shiga tsakani na kungiyar adawar kasar Syria Mohammed Alloush ya isa birnin Geneva don halartar zaman tattauna rikicin kasar ta Syria da ya lakume rayukan mutane sama da 250,000

Tsohon shugaban kungiyar 'yan tawayen Jaysh al-islam ta kasar Syria  marigayi  Zahran Alloush
Tsohon shugaban kungiyar 'yan tawayen Jaysh al-islam ta kasar Syria marigayi Zahran Alloush AFP
Talla

Wannan dai shine karon farko da Mohammaed Alloush ke halartar taron karkashin jagorancin musamman na Majalisar dinkin duniya Staffan de Mistura a birnin Geneva na kasar Switzerland, taron zai mayar da hankali ne baki daya akan samar da matsaya guda a kawo karshen rikicin Syria na sama da shekaru 5.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ‘Yan tawayen Syria sun mayar da martani kan dakarun gwamnatin kasar a jiya litinin a kusa da wata hanyar shigar da kayyaki cikin birnin Aleppo yayin da suka ce, babu kakkautawa a lugudan wutar da jiragen saman Rasha ke yi a kasar duk da alkawarin tattaunawar zaman lafiya da ke kasa.

Manzan musamman na majalisar dinkin duniya a Syria, Steffan de Mistura ya kara kaimi wajan gudanar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin yan adawa da gwamnati yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu suka haura 70 bayan harin kunar bakin wake da mayakan ISIL suka kaddamar a kusa da birnin Damascus.

Tattaunawar ta sulhu a Geneva na a matsayin yunkurin farko cikin shekaru biyu da aka yi da nufin cimma yarjejeniya dangane da rikicin kasar ta Syria wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 250,000 tare da tilasta wa miliyoyin jama’a kaurace kasar, inda suka haddasa wani yanayi mafi muni a tarihi sakamakon kwarraransu nahiyar kasashen Turai don samun mafaka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.