Isa ga babban shafi
Najeriya

Lassa: Kakar maganin Bera ta yanke saka a Najeriya

Kasuwar maganin Bera ta cira sama a Najeriya sakamakon barkewar cutar Lassa da ta fara zama annoba bayan mutuwar mutane kusan 80 a sassan kasar.

Cutar Lassa na ci gaba da yaduwa a Najeriya
Cutar Lassa na ci gaba da yaduwa a Najeriya barbaric.com
Talla

Ana kamuwa da cutar Lassa ne ta hanyar cin abincin da Bera ya gurbata da gubar bakin shi ko kuma mu’amala da wadanda ke dauke da cutar.

Rahotanni daga Kano sun ce kasuwar maganin bera ta cira sama bayan ruwaito mutane kimanin 17 sun kamu da cutar, da ke yin kisa.

Mutane na sayen maganin ne domin kashe beraye a gidajensu don gudun kamuwa da cutar Lassa, Kamar yadda shehu Idris Bichi shugaban ‘Yan kasuwar ta magani ya shidawa kamfanin dillacin labaran Faransa.

Sama da mutane 200 hukumar lafiya a Najeriyaya ta tabbatar da cewa suna dauke cutar.

An sanya wa Cutar sunan garin Lassa a cikin Jihar Borno inda aka fara samun bullarta a 1969.

Cutar Lassa yanzu ta bulla a Jihohi 17, kamar yadda ma’aikatar Lafiya ta tabbatar a Najeriya.

Tuni Gwamnatin Jihar Benue ta dauki matakin haramta cin bera a daukacin sassan Jihar a wani mataki na magance yaduwar cutar da ta bulla a Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.