Shekaru 50 da kisan su Sardauna da Tafawa Balewa
Yau juma’a 15 ga watan Junairu, shekaru hamsin kenan da akayi juyin mulki na farko a Najeriya, inda sojoji suka kashe Firaministan kasar Sir Abubakar Tafawa Balewa da Firamiyan jihar Arewa sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tun daga wannan lokaci har zuwa yanzu,yankin arewa da al'ummominta ba su farfado daga kidimewar da ta same su ba sakamakon wancan mummunan al'amari.
Da dama daga cikin yan kasar na ci gaba da alfahari da nasarorin da Gwamnatin lokacin ta samu tareda dora yankin arewa a kan tafarkin ci gaba da zaman lafiya.
An dai haifi Sa Ahmadu Bello a ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1910 a wani gari da ake kira Rabba a cikin jihar Sakkwato dake arewacin Najeriya.
Tarihi ya nuna cewa kakan sa shi ne Sarkin musulmi Malam Bello,wanda ya kasance daya daga cikin mutanen da sukka kafa daular Musulunci ta Sakkwato a wancan karnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu