Jean Ping na AU zai shiga takara a zaben Gabon
Tsohon Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU, Jean Ping ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar shugabancin kasar Gabon domin kawo karshen mulkin shugaba Ali Bongo.
Wallafawa ranar:
Ping ya ce bukatarsa ita ce kawo sauyi da yadda ake gudanar da shugabancin kasar don tabbatar da gaskiya da sanya wa’adin shugabancin da kuma zuba jari a bangaren kiwon lafiya da ilimi da kayan more rayuwa.
Ping dai na kokarin kawo karshen shekaru 50 da Jam’iyya mai mulki ta shafe tana shugabanci a Gabon.
A zaben 2009 ne Ali Bongo ya gaji Mahaifinsa Omar Bongo da ya rasu.
A watan Agusta mai zuwa ne za a gudanar da zaben kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu