Gwamnatin jihar Kano a tarayyar Najeriya ta bullo da wani shirin bunkasa noma ta hanyar taimakawa manoma da bashin da ba ya da ruwa.Manoma alkama, na daga cikin na farko da ke amfana da shirin, kuma Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da manoma da kuma hukumomi a jihar ta Kano dangane da wannan shiri.
Sauran kashi-kashi
-
Matsalar yoyon iskar gas yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha yankin Delta
Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023 wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa har zuwa wannan lokaci.04/05/202419:32 -
Matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka don magance matsalar tsuntsaye a gonaki
Shirin 'Muhalli' na wannan makon tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan tu’annatin da wasu nau'in tsuntsaye da ake kira jan-baki ke yi wa gonaki a Najeriya tare da kokarin da gwamnati ke yi domin shawo kan lamarin.20/04/202419:27 -
Najeriya ta kasance kan gaba a fagen noman masara a yankin yammacin Afrika
Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin.Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Taraba da kuma wasu ‘yan kalilan din jihohin kudu maso yammacin kasar.23/03/202421:02 -
Yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta
Shirin mu na wannan mako zai yi duba ne a kan batun yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta da ke tarayyar Najeriya musamman a jahar Cross River.Wakilin mu dake yankin MURTALA ADAMU ya kai ziyara a wa ta Gona da ake wannan kiwon kuma ya zanta da wadanda suke sana'ar, wa ta da ta rungumi sana'ar ta yi bayani dalla dalla yadda ake fara tsara kiwon da kuma abubuwa da suka dace a tanada.24/02/202417:26 -
Halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya
Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan batun halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya, tare da duba matakan da suke dauka na kare kai anan gaba.Idan ba a manta ba dai Shekara guda kenan da faruwa mummunar ambiyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, kuma jihar jigawa dake arewacin kasar na cikin jihohin da ambaliyar tayiwa barna10/02/202420:09