Afrika ta kudu za ta shigar da tan miliyan 5 na masara
Rahotanni daga kasar Afirka ta kudu sun ce kasar za ta shigar da tan miliyan 5 na masara domin cike gibin karancin abincin da ake fama da shi a kasar sakamakon matsalar farin da aka samu a kakar bana.
Wallafawa ranar:
Jannie de Villiers, shugaban hukumar samar da abinci a kasar ya danganta matsalar farin da aka samu da sauyin yanayi wanda ya sa aka yi asarar kusan ton miliyan 10 na masara da ake nomawa a kasar.
Jami’in ya ce kasar na cikin mawuyacin hali a yanzu haka.
Ko a watan jiya sai da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da matsalar abinci a daukacin kasashen da ke kudancin Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu