Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

Shekaru biyu da soma yaki a Sudan ta kudu

A yau 15 ga watan Disemba aka cika shekaru biyu da barkewar rikici a kasar Sudan ta kudu tsakanin dakarun gwamnatin Salva Kiir da masu biyayya ga tsohon mataimakinsa Riek Machar.

A 9 ga watan Yulin  2011 Sudan ta kudu ta samu 'Yancin kai daga Sudan
A 9 ga watan Yulin 2011 Sudan ta kudu ta samu 'Yancin kai daga Sudan REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Rikicin kasar ya soma ne bayan shugaba Kiir ya zargi Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa, daga baya kuma rikicin ya rikide ya koma na kabilaci tsakanin kabilun shugabannin biyu.

Sau takwas bangarorin biyu na rusa yarjejeniyar tsagaita wuta da suka amince a Addis Ababa domin kawo karshen rikicin kasar.

Sama da mutane 50,000 aka kiyasta sun mutu a rikicin, yayin da kuma rikicin ya raba sama da mutane Miliyan biyu da rabi da gidajensu.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane Miliyan hudu da rabi ke bukatar taimakon abinci a Sudan ta kudu a yanzu haka.

Kokarin da aka yi na kafa gwamnatin hadin kai tsakanin bangaren gwamnatin Salva Kiir da Riek Machar ya faskara, yayin da ‘Yan tawayen suka ki cim ma wa’adin da aka diba 24 ga watan Nuwamban shekarar nan akan su dawo Juba karkashin yarjejeniyar da suka amince.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.