An yi yunkurin halaka Burutai a Zaria
Sojojin Najeriya da kungiyar musulmi mabiya akidar Shi’a na zargin juna da haifar da rikicin da ya kai ga rasa rayukan mutane da dama a garin Zaria cikin Jihar Kaduna a jiya Asabar.
Wallafawa ranar:
Rundunar sojin Najeriya na zargin mabiya shi’a da yunkurin halaka babban hafsan sojin Kasar Janar Tukur Burutai a lokacin da ayarinsa ke kan hanyar zuwa fadar Sarkin Zazzau.
A yayin da kuma bangaren kungiyar Shi’a a Zaria ta musanta zargin tare da zargin sojin kasar da kashe mabiyanta ba wani dalili.
A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Sojin Najeriya Kanal Usman Kukasheka yace ‘Yan shi’ar sun toshe hanyar da babban hafsan Sojin zai wuce zuwa fadar Zazzau inda suka kona tayu dauke da adduna da duwatsu.
Kukasheka yace Sojoji sun kare kansu bayan mabiyan sun abkawa tagawar babban Hafsan sojin ta Najeriya Turkur Burutai.
Mutane da dama ne dai aka ruwaito sun mutu a arangamar da aka yi tsakanin Sojoji da mabiyan na Shi’a a garin Zaria.
Rundunar Sojin Najeriya tace an 'Yan Shi'a sun nemi halaka Janar Burutai a Zaria
SHIITE SECT ATTACKS CHIEF OF ARMY STAFF'S CONVOY https://t.co/6Qv02UBc3b
@skusman pic.twitter.com/F7NP2rUSex
— Nigerian Army (@HQNigerianArmy) December 12, 2015
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu