Isa ga babban shafi
Kogi

Yahya Bello ya lashe zaben Kogi

Hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da Yahya Bello na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kogi bayan kammala sauran zaben jihar a wasu muzabu 91 a jiya Assabar.

Yahya Bello ya lashe zaben Jihar Kogi
Yahya Bello ya lashe zaben Jihar Kogi scruterblog
Talla

INEC tace Yahya Bello na APC ya samu kuri’u fiye da Gwamna mai ci Idris Wada na Jam’iyyar PDP.

Yahya Bello shi ya maye gurbin Prince Abubukar Audu wanda ya rasu kafin a kammala zaben da aka gudanar a ranar 21 ga watan Nuwamba, lamarin da ya rikita lissafin siyasa a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.