Isa ga babban shafi
China-Africa

Xi Jinping na ziyara a Afrika

A yau talata Shugaban kasar China Xi Jinping ya isa kasar Zimbabwe, a wata ziyara irin sa na farko da ya kawo Afrika, inda zai ganawa da shugaba Robert Mugabe kan batutuwa bunkasar tattalin arziki, daga bisani kuma ya wuce Afrika ta kudu.

Shugaban kasar China Xi Jinping da na Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar China Xi Jinping da na Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Wannan dai shine karo na farko tun bayan shekarar 1996, da shugaban China ke kai ziyara Zimbabwe, kuma ana saran a ziyarar ta sa, ya sanya hannu kan yarjejeniya bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma samar da wadataccen wutan lantarki.

Zimbabwe da ke fuskantar wariya daga kasashen yammaci, tun lokaci da aka zargi gwamantin shugaban kasar Robert Mugabe da mugudin zabe da keta hakki bil’adama, na samun taimako China wajen zuba hanayan jari ciyar da kasar gaba da samar da kayayyakin more rayuwa ga al’ummar kasar.

Rahotanni na cewa bankunan Zimbabwe da hadin gwiwar na China za su baiwa gwamnati kasar, rancen sama da dala biliyan 1, domin gina cibiyar makamashi da zai ke samar da megawatt 600 na wutan lantarki a kasar.

Kana a gobe laraba kuma shugaba XI zai wuce Afrika ta kudu inda zai gana da Jacob Zuma da kuma halarta taron kasashen Africa da China da za a gudnar a Johannesburg.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.