Isa ga babban shafi
Vatican-Afrika ta tsakiya

Fafaroma ya ziyarci Masallaci a Afrika ta tsakiya

Fafaroma Francis ya yi wa’azi kan yafe wa juna da sasasantawa a ziyarar da ya kai a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya mai fama da rikicin addini, a yau Litinin kuma shugaban na Darikar Katolika ya ziyarci wani Masallaci a birnin Bangui kafin ya kammala ziyarar.

Shugaban mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya kai ziyara Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya mai fama da rikici
Shugaban mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya kai ziyara Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya mai fama da rikici REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Rahotanni sun ce Fafaroman ya kai ziyara Masallacin Koudoukou da ke unguwar PK5 domin ganawa da wasu limamai 5 kafin daga bisani ya yi wa sauran jama’ar Musulmin birnin jawabi.

Fafaroma yace zaman lafiya ba zai samu ba sai idan an yafewa juna.

Shugaban mabiya darikar katolikan zai kuma yi addu’a ga mabiyansa a filin wasan Boganda kafin ya koma zuwa fadar Vatican.

Wannan ne karon farko da Fafaroma ya kawo ziyara a wata kasa da ke fama da rikici musamman a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.