Kamaru
Mata sun kai harin kunar bakin wake a Kamaru
Akalla mutane 7 suka mutu a wasu hare haren kunar bakin wake da mata biyu suka kai a garin Dabanga cikin Arewacin Kamaru a jiya Assabar. Daga cikin wadanda suka mutu har da matan biyu ‘yan kunar bakin wake.
Wallafawa ranar:
Talla
Gwamnan yankin arewa mai nisa Midjiyawa Bakary, ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa akwai sojojin Kamaru biyu da suka samu rauni.
Wannan ne dai karon farko da aka kai hare haren kunar bakin wake a Dabanga da ke kusa da Kousseri kan iyaka da Najeriya.
Arewacin Kamaru dai na cikin yankin da mayakan Boko Haram na Najeirya suka addaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu