Mali
An kashe Sojojin MDD 3 a Mali
Kungiyar Mayakan Ansar Dine masu da’awar Jihadi a Mali ta yi ikirarin daukar alhakin harin roka da aka kai a sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Wallafawa ranar:
Talla
Mutane uku suka mutu a harin da suka kunshi Jami’an wanzar da zaman lafiya guda biyu da wani farar hula guda, sannan kimanin 20 suka jikkata a harin na Kidal.
Harin na zuwa ne duka mako guda da aka kai wani mummunan hari a wata Otel a Bamako babban birnin kasar Mali.
Majalisar Dinkin Duniya ta la’anci harin, yayin da kwamitin tsaro ya danganta harin a matsayin laifukan yaki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu