Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 21 suka mutu a harin da aka kai wa ‘Yan Shi’a a Kano

Akalla mutane 21 suka mutu a wani harin kunar bakin wake da wani ya kai a gangamin mabiya shi’a da ke tattaki daga Kano zuwa Zaria a arewacin Najeriya a ranar Juma’a.

Hare haren Kungiyar Boko Haram Boko Haram sun kashe mutane da dama a Najeriya
Hare haren Kungiyar Boko Haram Boko Haram sun kashe mutane da dama a Najeriya AFP/AFP/Archives
Talla

Dan kunar bakin waken ya tayar da bom din ne a Dakasoye cikin Jihar Kano, sannan wasu da dama ne suka jikkata a harin.

Rahotanni sun ce dan kunar bakin waken da ake has ashen Dan Boko Haram ne ya saje ne cikin mabiyan Shi’a kafin ya tayar da bom din.

A samu nasarar kame guda daga cikin maharan, kafin ya tayar da bom din da ya yi damara dashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.