Rwasa na zaman dari dari a Burundi
Shugaban ‘yan adawa na kasar Burundi, Agathon Rwasa ya ce yana gudun rasa ransa saboda yadda rikicin kasar ya tsananta bayan an zabi shugaba Pierre Nkurunziza a karo na uku.
Wallafawa ranar:
Rwasa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, a ko da yaushe yana zaman dari dari ne, abinda ke sa shi yawan sauya shirinsa na tafiye tafiye.
Rwasa ya kara da cewa, ana fakon sa a ko ina kuma bai san wanda zai iya yi masa kwantan bauna ba.
Rwasa dai ya bayyana haka ne a birnin Cape Town na kasar Afrika ta kudu, inda ya halarci wani taro kuma ya ce duk da barazanar da ya ke fuskanta hakan ba zai sa shi neman mafaka ba a Afrika ta kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu