Isa ga babban shafi
Kenya-Uganda-Vatican

Paparoma Francis yayi kira zuwa Shugabanin Duniya

Paparoma Francis ya bayyana cewar rashin samun nasarar taron sauyin muhallin da za’a gudanar a birnin Paris zai yi matukar illa ga al’ummar duniya.Yayin da yake jawabi a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya dake kula da muhalli a Nairobi, Paparoman yace duniya na fuskantar babar kalubalen da ya dace a dauki mataki akai, wanda ke nuna ko a dauki matsayin ceto muhallin ko kuma a lalata shi baki daya. 

Shugaban mabiya darikar Katolikan na Duniya Paparoma Francis.
Shugaban mabiya darikar Katolikan na Duniya Paparoma Francis. REUTERS/Tony Gentile
Talla

Paparoma ya zargi manyan kasashen duniya da kaucewa daukar nauyin da ya rataya akan su.
Shugaban mabiya darikar Katolikan na Duniya a wanan ziyara ta sa na sa ran gani abubuwa da dama sun canza a Duniya.
Ya na mai fatar gani an cimma zaman lahiya mai dorewa a wasu kasashen Afrika dake fama da yaki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.