Isa ga babban shafi
Kenya

Paparoma ya gana da shugabannin addinai a Kenya

Shugaban darikar Katolika ta duniya da ke ziyara a Afrika, Paparoma Francis ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin addinai za ta taka rawar gani wajan fahimtar da matasa cewa rikici da sunan addini kuskure ne.

Shugaban darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis a Kenya
Shugaban darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis a Kenya REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Paproman ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar a gaban dubban jama’a da suka yi cincirindo a babban birnin Nairobi na kasar Kenya, kuma dama an yi zaton zai yi magana game da hadin kai tsakanin mabiya addinin Islama da Krista.

Paproman ya fara ganawa da shugabanin addinan kafin daga bisanai ya jagoranci taron addu’ar da ya samu halartar dimbin jama'a, wadanda suka yi ta wake- wake da raye- raye duk da dukan ruwan saman da suka sha.

Papromann ya shaida wa shugabannin addinan cewa, ana sanya wa matasa ra’ayin rikau da sunan addini, abinda da ke kawo baraka a tsakanin al-umma, yayin da ya gargadi cewa dole ne a daina amfani da addini wajan haifar da tarzoma da kiyayya, yana mai tunawa da harin da kungiyar al-Shebab ta Somalia ta kai akan rukunin shaguna na Westgate a shekara ta 2013 a Nairobi da kuma Jam’iyar Garissa ta Kenya a cikin wannan shekarar.

Ziyarar ta shi za ta kai shi har kasashen Uganda da jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da ke fama da rikici.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.