Isa ga babban shafi
Gambia

Shugaban Gambia ya haramta yiwa ‘ya’ya mata Shayi

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya sanar da dokar hana yiwa ‘ya’ya mata shayi a cikin kasar, sanarwar dake zuwa a da-idai  lokacin da ake bikin ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya.

Shugaban Kasar Gambia, Yahya Jammeh
Shugaban Kasar Gambia, Yahya Jammeh Reuters/Lucas Jackson
Talla

A dai-dai wannan ranar 25 ga watan Nuwamban da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin yin nazari tare da fadakar da jama'a illolin da ke tattare da cin zarafin mata, shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya fito da sabuwar sanarwar hana yiwa yara mata shaye acikin kasar al’amarin da ya matukar farantawa al’umma ciki da wajen kasar rai.

Shugaba Jameh ya ce al’adar yiwa mata shayi ba abu ne da addinin musulunci ya yarda da ita ba ganin kashi 95 cikin 100 na al’ummar kasar musulmi ne.

Shugaban ya ce dokar ta soma aiki ne nan take daga yau laraba inda ya kuma gargadi iyaye da masu unguwanin a kauyukan kasar dake wannan al’ada da su bi dokar kokuma su fuskanci fushin hukuma.

Daga cikin matsalolin da ke tattare da yiwa yara mata shayi akwai yiyuwar zubar da jini da shigar kwayar cuta, a wasu lokutan kuma rashin gamsuwa a yayin Saduwa.

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ce mata sama da miliyan 125 aka yiwa shayi a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.