Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

MDD zata tura karin dakaru Sudan ta Kudu

Sakatare Janar da Majalisar dinkin duniya, Ban ki-Moon ya bukaci aikewa da karin dakarun wanzar da zaman lafiya dubu daya da dari daya Sudan ta kudu, domin kare rayukan fararan hula da ake cigaba da kaiwa hari duk da yarjejeniyar zaman lafiya da bangarori dake rikici da juna suka sanyawa hannu watanni 3 baya.

Sakatare Janar na MDD Ban ki-Moon
Sakatare Janar na MDD Ban ki-Moon 路透社照片
Talla

Mista Ban ya mika wannan bukatar ne a wani rahotan daya gabatarwa Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a makon daya gabata, wanda ke bayana karara yadda ake ci gaba da cin zarafin fararan hula duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a kasar.

Batun da ake gani akwai bukatar diga ayar tambaya kan wanna yarjejeniya, lura da cewa ta ki aiki a kasar, kuma abubuwa na sake daukan sabon fasali.

A yanzu dai buakatar Ban ki-Moon shine aike karin dakarun Soji 500 da ‘yan sanda 600 kasar, da jirage masu saukan angulu 13 wanda sojoji za suke amfani dashi.

Sakatare ya kuma bukaci kai taimako asibitin Bentiu, inda ‘yan gudun hijira kasar kusa dubu 100 ke sansani, tare da kuma gyara sha’ani kiwon lafiya a asibiti Juba, musamman fanin taimakon gaggawa.

Tun a shekarar 2013 Sudan ta kudu ta fada cikin yaki, lokacin da Shugaba Salva Kiir ya zargi mataimakinsa da yunkuri kitsa masa jiyun mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.