Isa ga babban shafi
Tunisia

Gwamnatin Tunisia ta kafa dokar ta baci

Shugaban kasar Tunisia Beji Essebsi ya kafa dokar ta baci da hana fitar dare bayan wani kazamin harin da aka kai kan motar da ke dauke da jami’an da ke tsaron fadar shuagban kasar wanda ya kashe 12 daga cikin su. 

Shugaban kasar Tunisia Beji Caïd Essebsi.
Shugaban kasar Tunisia Beji Caïd Essebsi. AFP PHOTO / FETHI BELAID
Talla

Shugaban kasar wanda ya soke tafiya zuwa Switzerland da ya shirya yi  a yau, ya sanar da kafa dokar ta baci a fadin kasar da kuma kafa dokar hana fita a birnin Tunis daga karfe 9 na daren jiya zuwa karfe 5 na asubahin yau.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin kuma tun a shekara ta 2011 kasar ke fuskantar hare haren ta'addanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.