Isa ga babban shafi
Algeria-Bakin haure

Gobara ta kashe Bakin haure 18 a Algeria

Hukumomin Kasar Algeria sun ce wata gobara ta tashi a sansani Bakin haure tare da kashe mutane 18, cikinsu hada kanana yara, yayin da wasu kusan 50 suka samu rauni.

Sansani Bakin haure
Sansani Bakin haure Reuters/路透社
Talla

Gobara ta tashi ne cikin dare sakamakon tar-tsatsin wutan lantarki a sansani da bakin haure sama da 650 ke mafaka a Ouargla mai nisan kilomita 800 daga kudancin Algeria.

A cewar Kanar Farouk Achour na kumar agajin gaggawa kasar, gobara ta tashi ne da misalin karfe 2 daren agogon GMT yara 2 da mata 3 ke cikin mutane 18 da suka mutu.

Kawo yanzu ba a iya tantace ko ‘yan wani kasa ba ne iftila’i ya ritsa dasu, sai dai akwai wasu 43 da suka samu munana kuna.

Shugabar hukumar agaji ta Red cresent dake kasar Saida Benhabiles ta shaidawa kamfanin dilanci labaran faransa AFP cewa karanci wutan lantarki ne ya haifar da gobarar, kuma a halin yanzu mutane 27 na cikin mawuyacin hali.

Hukumomin kasar dai sun shiga bincike domin tabbatar da gaskiyar wannan gobarar.

Tun a shekarar 2011 da rikicin libya ya yi zafi, Algeria dake da iyaka da Mali da Niger, ta zama kasar da Bakin haure dama ‘yan gudun hijira ke shiga domin neman mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.