Isa ga babban shafi
Nijar

An cafke Hama Amadou bayan ya dawo Nijar

Hukumomin Nijar sun cafke Hama Amadou dan takarar shugaban kasa a bangaren Jam’iyyar adawa a Jamhuriyyar Nijar bayan ya dawo kasar a yau Assabar.

Hama Amadou, a lokacin da yake shugabancin majalisar dokokin Nijar
Hama Amadou, a lokacin da yake shugabancin majalisar dokokin Nijar AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

An cafke Hama Amadou ne a lokacin ya ke sauka daga Jirgi a Yamai, inda ‘Yan sanda suka mika ma shi sammacin kama shi, kamar yadda lauyan da ke kare tsohon Firaministan kasar ya tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP.

A watan Agusta ne Hama Amadou shugaban Majalisar Nijar kuma babban mai adawa da shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya gudu zuwa Faransa domin gujewa fuskantar shari’a kan zargin mallakar ‘ya’yan da aka yi fataucinsu daga Najeriya.

Wannan dai babbar barazana ce ga Hama Amadou da magoya bayan shi a zaben shugaban kasa a 2016.

Tuni tsohon Firaministan kasar ya musanta zargin wanda ya danganta da yarfen siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.