Isa ga babban shafi
Nijar

An cafke shahararrun 'yan fashi a yankin Agadez

Rundunar ‘yan sandar jihar Agadez a jamhuriyar Nijar ta sanar da kama wasu mutane da suka shahra wajen aikata fashi da makami da kuma kisan jama’a a yankin.

Bakin haure a dajin Agadez jamhuriyar Nijar
Bakin haure a dajin Agadez jamhuriyar Nijar REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Rundunar ta ce mutanen na amfani da bindigogi domin yi wa jama’a kwace a cikin garin Agadez da kuma sauran yankuna, musamman ma tsakanin garin Agadez da Djado inda ake hako zinari.

An gano bindigogi da dama cikinsu har da makami mai linzame wato rocket, da kuma motocin wadanda ‘yan bindigar ke amfani da su wajen aikata miyagun laifufuka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.