PNDS ta tsayar da Issoufou a zaben Nijar
Jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki a Jamhuriyar Nijar ta bayyana shugaba Mahamadou Issoufou a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da za a gudanar a badi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Jam’iyyar PNDS Bazoum Mohamed yace sun yaba da jagorancin Issofou kuma sun amince ya ci gaba da jagorantar kasar domin ya samu damar idar da ayyukan da ya dauko don ci gaban ‘Yan Nijar.
Yanzu shugaba Issoufou shi ne na uku daga cikin ‘Yan takarar da suka bayyana kudirin tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Fabrairun 2016. Daga cikin ‘Yan takrarar kawai Hama Amadou babban mai adawa da Shugaba Issoufou da kuma tsohon Minista Amadou Boubacar Cisse, wadanda dukkaninsu suka marawa Issoufou baya a zaben 2011 zagaye na biyu.
Lydia Ado ta aiko da rahoto game da taron PNDS
Amma ana ganin zaben Nijar na badi zai kasance mafi inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira a gudanar da karbabben zabe cikin kwanciyar hankali, musamman yanzu da kasar ke fama da barazanar Boko Haram.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu