Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta soki kamfanin Shell

Manyan Kungiyoyin kare hakkin bil’adama a duniya sun soki kamfanin hakar mai na Shell game da ayyukan tsabtace muhallin da ya gurbata a yankin Neja Delta a Najeriya.

Mutanen Ogoni sun dade suna kalubalantar Shell kan gurbata muhullinsu a yankin Neja Delta na Najeriya
Mutanen Ogoni sun dade suna kalubalantar Shell kan gurbata muhullinsu a yankin Neja Delta na Najeriya AFP PHOTO
Talla

Kungiyar Amnesty ta zargi Kamfanin da rashin aiwatar da shawarwarin da aka tsara a rahoton Majalisar Dinkin Duniya na 2011.

A cikin wani sabon rahoto da Amnesty ta fitar tare da hukumar kare hakkin bil’adama da ci gaba CEHRD, sun ce babu wani aiki da kamfanin Shell ya gudanar na tsabtace muhallin mutanen Oginiland da aka gurbata.

Yanzu haka mutanen yankin da ‘yan rajin kare muhalli sun shirya gudanar da wata zanga-zanga a makon gobe daidai da cika shekaru 20 da kisan Ken Saro-Wiwa domin nuna adawa da kamfanin Shell.

Amnesty tace daga cikin wurare 13 da ta ziyarta cikin 15, tsakanin watan Yuli zuwa Satumba babu inda Kamfanin Shell ya gudanar da aikin tsabtace muhallin mazauna yankin.

Tun a 2008 ake zargin kamfanin Shell da zubar da man da yawan sa ya kai ganga 4,000 wanda ya gurbata yanayi da abinci a Yankin Ogoniland musamman kifayen da mutanen yankin suka dogara da shi.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da kafa wani asusu domin daukan nauyin tsaftace yankin Ogoni a Neja Delta mai arzikin mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.