ICC ta dage shari'ar Laurent Gbagbo
Kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya ICC, ta dage shari’ar da ake yi wa tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo zuwa ranar 28 ga watan Janairu na shekara mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Kotun ta ce ta dage sauraron karar zuwa shekara mai zuwa ne domin bai wa alkalan kotun nazari kan bayanan lafiyar tsohon shugaban.
Matsayin kotun na zuwa ne ranar da hukumar zaben Coted’Ivoire ta bayyana Alassane Ouattar a matsayin wanda ya lashe zaben kasar.
Ana tuhumar Gbagbo mai shekaru 70 bisa aikata lainfin cin zarafin al-umma bayan ya haifar da rikicin siyasa lokacin da ya ki amince wa da shan kayi a takarar da ya yi da Ouattara a shekara ta 2010.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu