Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram ta kashe Sojojin Nijar biyu a Diffa

Sojojin Nijar biyu aka kashe a harin kunar bakin wake da mayakan Boko Haram suka kai a wani kauye da ke cikin yankin Jihar Diffa a kudu masu gabashin kasar a yau Laraba.

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Maharan sun kai harin ne a kauyen Blangouri da ke kusa da garin Diffa a cikin dare.

Ministan tsaron Nijar Mahamadou Karidjo ya ce jami’an tsaron kasar sun yi nasarar kashe ‘Yan ta’addan tare da tarwatsa makamansu. Amma a cewarsa Sojojin Nijar biyu suka mutu kuma wasu sun samu rauni.

Boko Haram dai ta jima tana kai hare hare a yankin Diffa da ke cikin dokar ta-baci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.