Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Za a gudanar da bicinke kan kisan mutane dama juyin mulki a Burkina Faso

Gwamnatin Kasar Burkina Faso ta kadamar da bincike kan juyin mulkin da akayi a kasar don gano daukacin masu hannu a ciki nan da kwanaki 30 masu zuwa.

Michel Kafando shugaban wucin gadin kasar Burkina Faso
Michel Kafando shugaban wucin gadin kasar Burkina Faso REUTERS/Arnaud Brunet
Talla

Firaminsitan kasar Isaac Zida ya bayyana cewar hukumar binciken shari’a a karkashin alkalin kotun daukaka karar kasar zata mayar da hankali kan wadanda suka shirya juyin mulkin, wadanda suka aiwatar da kuma sojoji da fararen hular dake da hannu a ciki.

Cikin wadanda ake saran yiwa tambayoyi harda Janar Gilbert Diendere shugaban juyin mulkin da Djibril Bassole tsohon ministan harkokin wajen kasar a karkashin gwamnatin Blaise Compaore.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.