Chadi ta tabbatar da mutuwar mutanen 41 a harin Baga Sola
Gwamantin Kasar Chadi ta sanar da cewar mutane 41 ne suka mutu sakamakon hare- haren da kungiyar Boko Haram ta kai kasuwar Baga Sola da ke kusa da iyakar Najeriya, yayin da wasu 48 suka samu raunuka.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotanni sun ce an kai harin ne a kasuwa da kuma sansanin 'yan gudun hijira da suka tserewa garuruwan su saboda hare-haren kungiyar.
Yanzu haka hukumomin lafiya na ci gaba da kula da wadanda suka samu raunuka a harin.
Kungiyar Boko Haram sun sake kai wasu jerin hare-hare a garin Kangaleri da ke da nisan kilometa 30 da garin Mora a kasar Kamaru a jiya lahadi.
Gwamnatin Kamaru ta bayana alhini ta, a cewar kakakin Gwamnatin kasar Issa Tchiroma wanda ya ce kungiyoyin fararen hula su bayar da hadin kai ga hukuma domin kawo karshen ta'adanci a kasashen Tafkin Chadi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu