Isa ga babban shafi
Central Africa

Shugaban Afrika ta Tsakiya na neman a karbe Makamai daga Jama'a

Shugaban kasar Janhuriyar Africa ta Tsakiya Uwargida Catherine Samba-Panza ta nemi hadin kan Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake kasar, da su taimaka domin ganin al’umomin kasar sun ajiye dukkan makamai dake hannun su.

Catherine Samba-Panza, Shugaban riko na kasar Afrika ta Tsakiya
Catherine Samba-Panza, Shugaban riko na kasar Afrika ta Tsakiya AFP PHOTO / TIMOTHY A. CLARY
Talla

Wannan kira na zuwa ne bayan hasarar rayukan mutane sama da 40 sakamakon tarzoma na addini da ta barke na baya-bayan nan a birnin Bangui.

Gidaje da dama aka kona, yayin da mutane sama da 40,000 suka rasa muhallin su.

Shugaban kasar ta fadi cewa al'ummar kasar na bukatar ganin an baiwa Rundunar Sojan wanzar da zaman lafiya da ke kasar karin karfi domin kwace dukkan makamai dake hannun jama’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.