Isa ga babban shafi
Mali

'Yan Tawayen Mali sun gana da Shugaban Kasar kan sulhu

Tawagar ‘yan tawayen arewacin kasar Mali ta gana da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita a birnin Bamako, tare da amincewa da ci gaba da halartar tattaunawa a karkashin kwamitin samar da zaman lafiya na kasar.

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta.
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta. AFP PHOTO/SEYLLOU-GEORGES GOBET
Talla

A cikin makonnin da suka gabata, ‘yan tawayen sun janye daga wannan kwamiti, bayan da wasu mayakan sa-kai da ke marawa gwamnati baya sun yi nasarar kwace wasu muhimman yankuna daga ‘yan tawayen.

Duk da cewa bangaren gwamnati da na ‘yan tawaye sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Algier na kasar Aljeriya, to amma har yanzu aiwatar da ita ya gagara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.