Isa ga babban shafi
Masar

Shugaban Masar ya yiwa ma'aikatan Al-jazeera afuwa

Shugaban kasar Masar Abdoul Fatah Al-Sisi a yau laraba ya yiwa Ma’aikatan talabijin na Aljazeera guda biyu da ke tsare a gidan yarin kasar afuwa.

Mohamed Fahmy da Baher Mohamed
Mohamed Fahmy da Baher Mohamed AFP PHOTO / KHALED DESOUKI
Talla

Afuwan da shugaba Abdoul Fatah Al-Sisi ya yiwa Mohammade Fahmy da Baher Mohammed abune da bama kafar Yada labaran Aljazeera kadai ke farin ciki da shi ba domin a yau laraba magoya bayan ‘yan jaridun da kungiyoyi kare hakin bil’adama da suka dadde suna ta fafutuka na ganin an saki ‘yan jaridan sun bayyana matukar farin cikin su.

‘Yan jaridan biyu da suka sami rakiyar ma’aikatan gidan yarin kasar zuwa tsakiyar birnin alkhahira sanyen da kayan gidan yari sun bayyana farin ciki da kuma mamakin matakin da shugaban kasar ya dauka na sakin su tare da wasu fursunoni dari daya.

Sai dai a cewar kakakin gwamnati kasar yace gwamnati ta yi hakan ne a jerin ayyukan alfarma a wannan lokaci na bikin sallah babba.

Tun a shekara 2013 ne wata kotu a kasar ta Masar ta yankewa ma’aikatan talabijin na Aljazerra hukuncin zaman gidan yari bisa laifin yada labaran karya a kasar dake fama da tashe tashen hankula.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.