Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Juyin mulki: Macky Sall na Senegal ya isa Burkina Faso

Shugaban kasar Senegal Macky Sall wanda ke shugabancin kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka Ecowas, ya isa birnin Ougadougou na kasar Burkina Faso, domin ganawa da sojojin da suka kwaci mulki a kasar, kuma za a yi wannan ganawa ne tare da shugaba Bony Yayi na jamhuriyar Benin.

Shugaban Kasar Senegal Macky Sall da sabon Shugaban Kasar Burkina Faso, Gilbert Diendere a lokacin ta ya tarbi Macky Sall a filin jiragen sama.
Shugaban Kasar Senegal Macky Sall da sabon Shugaban Kasar Burkina Faso, Gilbert Diendere a lokacin ta ya tarbi Macky Sall a filin jiragen sama. AFP PHOTO / AHMED AUOBA
Talla

Ziyarar ta shugaba Macky Sall, na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da sojojin suka sanar da bude iyokokin kasar, tare da cewa sun saki shugaban gwmanatin rikon kwarya Michel Kafando, to sai dai firaministansa Isaac Zida zai ci gaba da kasancewa karkashin daurin talala.

Macky Sall dai ya kasance shugaban wata kasa na farko da ya je Ouagadougou bayan faruwar wannan juyin mulki, yayin da majiyoyin diflomasiyya ke cewa shugaban na dauke da wani muhimmin sako daga kungiyar ta yammacin Afirka.

Hukumomin mulkin sojin sun bayyana cewa kofarsu a bude take domin shiga tattaunawa da ‘yan siyasa da kuma wakilan kungiyoyin fararen hula na kasar.

Hakazalika an tsara shugaban na Kungiyar ECOWAS-Cedeao zai gana da wakilan kungiyar tarayyar Afirka da na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da ake ciki a Burkina Faso domin samar da mafita dangane da wannan halin da kasar ke ciki.

To sai dai jagoran kungiyoyin fararen hular da suka gudanar da zanga-zamgar da ta yi sanadiyyar faduwar gwamnatin Blaise Campoare, Maitre Guy-Herve Kam, ya bayyana cewa ba wani sulhun da za a yi da sojojin illa fito na fito sai zuwa lokacin da suka mika mulki a hannun gwamnatin da suka ce sun kifar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.