Isa ga babban shafi
Saliyo-Ebola

Kasar Saliyo ta killace mutane dubu daya saboda Ebola

Mahukuntan Kasar Saliyo sun killace wani kauye dake kunshe da mutane sama da dubu daya a yankin kan iyakar kasar da kasar Guinea sakamakon mutuwar wata mata mai shekaru 67 bayan ta kamu da cutar Ebola.

Jami'an dake yaki da cutar Ebola.
Jami'an dake yaki da cutar Ebola. AFP Photo/Dominique Faget
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa killace kauyen mai suna Kambia da mahukuntan kiyon lafiyar kasar suka yi, na cikin tsatssauran matakan tsaron magance cutar kuma matakan sun hada da sanya dokar hana mazauna kauyen kai kawo daga wancan gidan zuwa wancan.

Har ila yau an baiwa ‘yan sanda da sojoji damar leka gida gida domin binciken gano wanda ke dauke da cutar a kauyen.

Yanzu haka dai hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da Ofishin Ministan kiwon lafiyar kasar ta Saliyo sun shirya gudanar da wani shirin yi wa duk mutanen da suka hadu da matar kafin mutuwarta allurar riga kafin cutar ta Ebola.

 

Za a iya cewa dai, wannan wani babban koma baya ne ga kasar ta Saliyo, wadda a makon da ya gabata ta sanar da warkewar mutum na karshe da ya kamu da cutar Ebola a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.