Liberia ta sake kubuta daga cutar Ebola
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta sake bayyana cewa Kasar Liberia ta kubuta daga cutar Ebola.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta sanar da haka ne a yau Al-hamis bayan kwanaki 42 da aka gudanar da bincike kan mutum na karshe da ake zaton na fama da cutar.
A watan Mayun daya gabata ne Hukumar lafiyar ta ce Liberia ta kubuta daga cutar yayin da ta sake bullowa bayan makwanni 6 da sanarwar.
Hukumar dai ta yaba da kokarin da Liberia ta yi na daukan matakan gaggauwa domin yakar cutar bayan mutane 6 su kamu da ita tare da kashe mutane 2 dabam.
Kasar Liberia dai na cikin jerin kasashen yammancin Afrika da cutar ta fi yiwa illa tun loacin da ta yadu sosai a shekarar 2013 , inda ta kama mutane dubu 28 tare da kisan sama da mutane dubu 11 a kasashen Guinea da Saliyo harma da Liberia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu