Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta dakatar da wani Liman kan Sallah ta fi Facebook a Kiran Sallah

Mahukuntan Masar sun dakatar da wani Limamin Masallaci bayan wasu mazauna kauyen da ya ke Limanci sun zarge shi da fadin Sallah ta fi Facebook maimakon Al’adar Sallah ta fi bacci, a kiran Sallar Asuba.

Masallacin Al-Azhar, na Masar
Masallacin Al-Azhar, na Masar Reuters / Amr Abdallah Dalsh
Talla

Limamin mai suna Mahmud Al Moghazi ya karyata zargin bayan kauyawan garin Behiera da ke lardin arewacin birnin Al Kahira sun kai karar shi ga mahukuntan Masar.

Ma’aikatar cikin gida a Masar tace, lamarin ya faru ne a ranar Assabar kuma tuni aka dakatar da Limamin.

Al Moghazi ya ce sharri ne ‘yan kungiyar Brotherhood suka yi ma shi saboda tsanarsa da suka yi don ya hana Kungiyar gudanar da ayyukansu a Masallacin.

Amma wasu na ganin Malamin yana neman gogawa Brotherhood kashin-kaji ne saboda jan hankalin gwamnati da ke karya ayyukan kungiyar.

Yanzu haka Malamin ya shiga yajin cin abinci don tabbatar da sharri ne aka yi ma shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.