Isa ga babban shafi
Masar

Kotun masar ta yanke wa 'yan jaridan Aljazeerah hukuncin dauri

Wata Kotun kasar Masar ta yanke wa wasu ‘yan jaridan gidan Talibijin din Aljazeerah hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari, bayan da tace sa samesu da baza labarun karya.

'Yan Jaridan Aljazeerah da aka yanke wa hukuncin dauri a Masar
'Yan Jaridan Aljazeerah da aka yanke wa hukuncin dauri a Masar REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

Dan kasar Canada Mohamed Fahmy da mai tsara shirye shirye Baher Mohamed dan kasar Masar suna kotu lokacin da aka yanke hukuncin, sai dai an yanke wa dan jaridan kasar Australia Peter Greste hukuncin a baya idonsa, sakamakon mika shi zuwa kasarsa da aka yi, a farkon wannan shekarar.
Akwai wasu mutanen da dama, da ake zarginsun da hade kai da mutanen, da suma aka yanke musu irin wannan hukuncin.
Tuni kasashen duniya suka yita Allah wadai da hukuncin, inda Canada ta nemi a gaggauta mayar mata da dan kasarta Mohamed Fahmy.
Cikin watan Disamban shekarar 2013 aka kama ‘yan jaridan, watanni bayan sojan kasar sun kifar da gwamnatin tsohon shugaba Mohamed Morsi.
A farkon wannan shekarar aka bayar da umarnin sake shari’ar, bayan da wata kotun daukakak kara tayi watsi da hukuncin farko, na daurin shekaru 7 a gidan yari, inda tace masu gabatar da kara basu da gamsassun shaidu.
Lauyan Fahmy, Amal Clooney, tace zata nema masa afuwar shugaban kasar ta Masar.
Lokacin da take jawabi a birnin Doha, lauyar gidan talibijin din na Aljazeerah, Farah Muftah, tace zasu daukaka kara kan hukuncin na jiya Asabar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.