An kama Shugabannin Boko Haram a Najeriya
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS a Najeriya ta ce ta cafke wasu manyan jiga-jigan Boko Haram da wasu ‘yayan kungiyar a sassa daban daban da suka hada da Lagos da Enugu a kudancin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumar ta fadi a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa ‘yayan kungiyar Boko Haram na kokarin tsallakawa zuwa Lagos domin ci gaba da kai hare haren ta’addanci.
Hukumar tace tun a watan Agusta ta kame ‘Yan Boko Haram da dama a Jihohin Lagos da Enugu da Kano da Bauchi da kuma Jihar Filato
Hukumar DSS ta bayyana cewa, daya daga cikin Kwamandojin da ta cafke akwai wanda ake kira Usman Shu’aibu da aka fi sani da suna Money, kuma ya tabbatar da cewa, shi ne shugaban wani gungun yan Boko Haram 9, da aka aiko daga dajin Sambisa domin aiwatar da hare haren kunar bakin wake a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu