Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi ta aiwatar da hukuncin kisa akan kwamandojin Boko Haram goma

Hukumomin Kasar Chadi a yau asabar sun aiwatar da hukuncin kisa kan wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram goma da aka yankewa hukuncin kisa a kasar.

REUTERS/Morteza Nikoubazl
Talla

Rahotanni daga birnin Ndjamena sun ce yau asabar ne aka harbe mayakan wadanda aka samu da laifin harin da ya kashe mutane 38 da kuma raunana wasu 100.

Kasar Chadi dake makwabtaka da Najeriya na daya daga cikin kasashen yankin dake fama da matsalar kungiyar Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.