Isa ga babban shafi
Chadi-Najeriya

Chadi ta zartar da hukuncin Kisa kan Mayakan Boko Haram

Kotun Kasar Chadi ta zartar da hukunci kisa kan  wasu mutane 10 masu alaka da kungiyar Boko Haram bayan ta same su da hannu a hare haren da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 38 a birnin N’Djemena a cikin watan Yunin da ya gabata. 

Boko Haram ta kashe mutane da dama a Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi
Boko Haram ta kashe mutane da dama a Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi REUTERS/Moumine Ngarmbassa
Talla

Wannan ne karo na farko da Kasar ta yanke irin wannan hukuncin kan 'yan kungiyar ta Boko Haram mai tada kayar baya a Arewa maso gabashin Najeriya.

Cikin wadanda aka yanke wa hukuncin har da wani dan Najeriya mai suna Mahamat Mustapha wanda aka fi sani da Bana Fanaye kuma kamar yadda hukumomin Chadi suka sanar, shine wanda ya kitsa harin kunar bakin waken da Boko Haram ta kai a ranar 15 ga watan Yunin daya gabata a wata makaranta da kuma ginin Yan Sanda a Kasar ta Chadi.

Kasashen Chadi da Najeriya da Kamaru masu makwabtaka da juna na fama da hare haren maytakan Boko Haram, yayin da a farkon wannan shekarar ne suka kafa rundunar hadin gwiwa domin yaki da Kungiyar wadda ta kashe akalla, muatane dubu 15 tun daga shekara 2009.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.