Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Burutai ya tsallake rijiya da baya

Babban Hafsan sojin kasa a Najeriya Lt. Janar Tukur Burutai ya tsallake rijiya da baya lokacin da mayakan kungiyar Boko haram suka budewa tawagar motar sa wuta yayin da ya ke ziyara garuruwan da sojojin Najeriya suka kama daga mayakan a Mafa da Dikwa.

Ziyarar tawagar Lt. Janar Tukur Buratai a kauyekan Borno
Ziyarar tawagar Lt. Janar Tukur Buratai a kauyekan Borno NIGERIA ARMY
Talla

Mayakan sun budewa tawagar ta sa wuta ne dauke da manya makamai, sai dai anyi nasara kasha 10 tare da cafke wasu 5.

A cewar sojin Najeriya sun rasa soji guda, yayin da wasu 4 suka jikata.

Hare-hare Mayakan Boko Haram dai a kauyekan jihar Borno da jihohi biyu da ke makwabtaka da ita na sake kamari.

Harin Mayakan ba a Najeriya kawai ya tsaya ba, har zuwa kasashen da ke makwabtaka da kasar da suka hada da Kamaru da Chadi.

A cikin watanin 3 sama da mutane dubu 1 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Kungiya.

Batun ta’addanci a Najeriya na daga cikin batutuwan da sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban ki-Moon zai mayar da hankali a ziyarar da ya kai Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.