Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kwance bama-bamai a titin Gwoza

Rundunar Sojin Najeriya da ke yaki da mayakan Boko Haram ta ce Sojojinta sun yi nasarar kawar da bama-bama da Mayakan Boko Haram ta dasa akan hanyar Gwoza zuwa Yamteke a cikin Jihar Borno.

Kwamandan Askarawan Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai
Kwamandan Askarawan Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai nigerian defence
Talla

Mai Magana da yawun rundunar Sojin ta 7 Kanal Tukur Isma’il Gusau ya ce Sojojin sun lalata bama-bamai biyar da kungiyar ta dasa a kan titin da ya hada Gwoza da Yamteke.

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta kuma ce yanzu suna ci gaba da aiki a Dikwa inda dakarun na Najeriya suka samu nasarar kama makamai da dama bayan sun kwato garin daga hannun Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.