Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Julius Malema na Afrika ta kudu ya bukaci kotu ta sake shi

Dan adawan kasar Africa ta Kudu Julius Malema, da ke fuskantar zargin cin hanci tsawon shekaru, ya nemi kotu ta sake shi, bayan da aka sake dage shari’ar da ake masa.

Julius Malema
Julius Malema Reuters
Talla

Ana zargin Malema, da ke jagorantar Jam’iyyar adawa ta EFF, da halarta kudaden haram, cin hanci da yin sama da fadi da kudaden da suka kai dalar Amurka Miliyon 5, shekaru 6 da suka gabata, lokacin da ya ke rike da mukamin shugaban bangaren matasa na jam’iyyar ACN.

Malema ya tsaya kai da fata kan cewa zarge-zargen ba wani abu bane illa bita da kulli daga tsofaffin abokan tafiyar shi na jam’iyyar ta ANC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.