Isa ga babban shafi
Najeriya

Bankin GT ya dakatar da karbar kudaden waje a Najeriya

Guranty Trust Bank ya dakatar da karbar kudade a asusunn ajiyar kudaden waje kuma matakin zai fara aiki daga yau Litinin 3 ga watan Agusta a a cibiyoyin bankunan na Najeriya har zuwa wani lokaci.

One of Guaranty Trust Bank Branch in Nigeria
One of Guaranty Trust Bank Branch in Nigeria tlcafrica.com
Talla

Bankin GT ya tura wa kwastamominsa sakon dakatar da karbar roron kudaden, kuma bankin ya ce ya dauuki wannan mataki ne don dakile hanyar boye kudade.

Sannan a karkashin matakin mutum ba zai iya aikawa da kudaden na waje ba ta hanyar Intanet sai dai ya je cikin Banki ya karbi tsabar kudin.

Amma daga kasar waje ana iya turawa mutum kudi a asusun ajiyarsa na kuudaden waje.

Haka ma wasu bankunan ‘yan kasuwa a Najeriya sun bbayyana matakin dakatar da karbar kudin dalar Amurka na ajiya.

Bankunan sun sun dauki matakin ne saboda yadda mutane ke sayen dala su ajiiye.

Kamfanin dillacin labaran Reuters ya ruwaito babban jami’in gudanarwar bankin First City Monument, Ladi Balogun, yana tabbatar da daukar matakin.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin da Naira ke ci gaba da faduwa da kusan kashi 16 a shekarun baya, a yayin da mutane suka koma zuba jari a dala suna ajiye wa a Banki.

A Najeriya dai ana sayar dala kusan naira 240.

Wasu ‘yan kasuwa a Najeriya sun bukaci babban bankin kasar ya dauki mataki akan bankunan da suka daina karbar tsabar kudin na dala a asusun ajiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.