Isa ga babban shafi
Burundi

An kashe tsohon babban kwamandan askarawan Burundi

An kashe wani babban Janar din sojin Burundi, kuma na hannu daman Shugaban kasar Pierre Nkurunziza a wani harin rokoki da aka kai masa a birnin kasar na Bujumbura.Lamarin da a yanzu ya haifar da tsoron sake samun barkewar rikici a kasar.

REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Jamia’an ‘yan sanda da kuma shaidun gani da ido sun ce da farko sai da aka fara harba wasu rokoki 2 a kan motar Janar din mai sunan Adolphe Nshi-miri-mana kana daga baya aka bude masa wuta a safiyar yau lahadi, inda aka yi nasara kashe shi tare da direban da ke tuka shi.

Tuni dai fadar gwamnatin kasar ta tabbatar da mutuwar Janar din, wanda tsahon babban kwamanda asakarawa sojojin kasar ne.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da wadanda suka kai harin ba, dake zuwa sama da sati guda da sanar da Nkurunziza a matsayin wanda ya samu nasara zaben kasar da aka gudanar a wani wa'adi na uku a jere.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.