Isa ga babban shafi
Najeriya

Wata ta kai harin kunar bakin wake a Maiduguri

Wata ‘Yar kunar bakin wake ta tayar da bom a kasuwar Gamburo kwastam a garin Maiduguri cikin keke Napep da safiyar yau Juma’a. Wakilin RFI Hausa Bilyaminu Yusuf wanda ya tabbatar da harin yace an samu hasarar rayuka.

Mata ke kai hare haren Kunar Bakin wake a Najeriya
Mata ke kai hare haren Kunar Bakin wake a Najeriya AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Bilyaminu ya ce kimanin mutane biyar suka mutu tare da jikkata wasu da dama, kuma adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.

‘Yar Kunar bakin waken ta kai harin ne sanye da hijabi cikin karamar mota mai kafa uku da ake kira Keke napep.

Zuwa yanzu Jami’an tsaro sun killace inda aka kai harin a garin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.