Isa ga babban shafi
Najeriya

An kwato Mutane sama da 50 a hannun Boko Haram

Rundunar sojan Najeriya da ke aikin wanzar da tsaro a yankin Arewa maso gabashin kasar mai fama da ayyukan Boko Haram ta sanar da ceto mutane 59, yawancinsu mata da kananan yara daga hannun kungiyar Boko Haram.

Sojojin Najeriya sun ceto mutane sama da 50 daga hannun Boko Haram
Sojojin Najeriya sun ceto mutane sama da 50 daga hannun Boko Haram (AFP Photo via yahoo
Talla

Kakakin rundunar Kanar Tukur Gusau ya ce an kubutar da mutanen ne a sansanin ‘Yan Boko Haram a Konduga cikin Jihar Borno a ranar Laraba.
Kuma cikin wadanda aka kubutar akwai mata 29 da yara kanana 25 da wasu maza masu manyan shekaru.

Wannan na zuwa ne bayan rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kubutar da wasu mutane 30 a makon da ya gabata.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International tace akalla mata 2,000 kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya tun farkon shekarar da ta gabata, cikinsu har da ‘Yan Matan garin Chibok sama da 200.

Kungiyar tace mayakan Boko Haram suna lalata da wasu ‘yan matan, tare da tursasa mu su daukar makamai.

Yanzu haka kuma Mata ne ke kai hare haren kunar bakin wake a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.