Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Janar Abbah zai jagoranci rundunar hadin guiwa

Najeriya ta nada Janar Iliya Abbah a matsayin sabon kwamandan rundunar hadin guiwa ta kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da Benin da za ta yi yaki da mayakan Boko Haram.

Sojin Najeriya da ke fada da Boko Haram
Sojin Najeriya da ke fada da Boko Haram AFP PHOTO/HO/NIGERIAN ARMY
Talla

Kakakin rundunar Sojin Najeriya Janar Chris Olukolade ya fadi a cikin wata sanarwa, cewa Manjo Janar Iliya Abbah ne sabon jagoran rundunar  hadin guiwa da ta kunshi dakaru 8,700 ta kasashe hudu masu makawabta da Najeriya da za su yi yaki da Boko Haram.

Janar Abbah ya taba jagorantar rundunar Najeriya a yankin Neja Delta mai fama da rikici.

Nan ba da jimawa ba ne rundunar hadin guiwar da ke da shalkwata a birnin N’Djamena na Chadi za ta kaddamar da yaki domin murkushe mayakan Boko Haram da suka addabi Najeriya da makwabtanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.